Tanzaniya na ci gaba da samun karin ayyukan zuba jari yayin da kasar Sin take kan gaba
2024-08-21 10:56:46 CMG Hausa
Cibiyar Zuba Jari ta kasar Tanzaniya ko TIC ta ce, Tanzaniya na ci gaba da samun karin ayyuka masu jawo zuba jari daga kasashen waje, yayin da ta samu ayyuka 490 da darajarsu ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 4 a cikin watanni bakwan farko na bana, kuma kasar Sin ke kan gaba.
Cibiyar ta TIC ta ce, ayyukan sun hada da noma, gine-ginen wuraren kasuwanci, makamashi, ababen more rayuwa na tattalin arziki, cibiyoyin hada-hadar kudi, habaka kwarewar ma’aikata, masana’antu, hakar ma’adinai da man fetur, hidimomi, sadarwa, yawon bude ido, da sufuri.
Kasar Sin ta kasance kan gaba a jerin manyan kasashe 10 masu zuba jari na ketare daga shekarar 1997 zuwa 2024, tare da gudanar da ayyuka 1,360 da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 11.5, wanda ya samar da guraben aikin yi 155,596, a cewar cibiyar ta TIC. (Mohammed Yahaya)