logo

HAUSA

Zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Vietnam ya samu sabuwar bunkasuwa

2024-08-21 10:17:04 CMG Hausa

A tsakanin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, idan muka ambaci kalmar abokai da ‘yan uwa, tabbas za a tuna dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Vietnam. Kwanan baya, shugaban kasar Vietnam To Lam, ya yi ziyarar aiki a kasar Sin, kuma wannan shi ne karo na farko da shugaban ya yi ziyarar aiki a kasashen waje, bayan ya fara aiki a matsayin shugaban kasa a farkon watan Agustan nan, lamarin da ya nuna muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Vietnam.

A ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaba To Lam. A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da kasar Vietnam gaban sauran kasashen dake kewaye da ita, a fannin raya huldar diflomasiyya. A nasa bangare kuma, shugaba To Lam ya ce, kasar Vietnam ta mai da dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin a matsayin babban tsarinta a fannin raya huldar diflomasiyya tsakaninta da kasashen waje.

Masana na ganin cewa, ra’ayoyin bangarorin biyu sun nuna zumunci mai daraja a tsakanin kasashen biyu, yayin da ake nuna aniyar kasashen biyu wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a wannan muhimmin lokaci na neman bunkasuwa da farfadowar kasashen biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)