logo

HAUSA

Sin Da Afirka Na Kokarin Neman Ci gaba Tare Cikin Hadin Gwiwa

2024-08-21 07:31:43 CGTN Hausa

Za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin daga ranar 4 zuwa ta 6 ga watan Satumba. Ana sa ran taron zai kunshi halartar shugabannin kasashen Afirka, da wakilai daga kasashen Afirka, da kungiyoyin yanki da na kasashen Afirka da ke da hannu a ayyukan da suka shafi taron. Manufar ita ce inganta ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka, inda dandalin ya kasance daya daga cikin hanyoyin gudanar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da kuma kara ingantata, yayin da bangarorin biyu ke kokarin kara karfafa alakar dake tsakaninsu.

Taron, mai taken "Hada Hannu don Ci Gaban Ayyukan Zamanantarwa, da Gina Babban Al'ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma ta bai daya," na da nufin samar da sabbin hanyoyin hadin kai da hadin gwiwa, ta yadda za a kara saurin bunkasuwar bangarorin biyu. Ana sa ran taron zai duba hanyoyin karfafa zumunci da hadin gwiwa da kuma rubuta wani sabon babi na gina al'ummar Sin da Afirka mai makoma bai daya. Wato a gudu tare a tsira tare da samun ci gaba tare ta hanyar hadin gwiwa. 

Tun lokacin da aka kafa wannan dandalin tattaunawa a shekarar 2000, an mai da hankali sosai kan samun da wadata tare da samun ci gaba mai dorewa ga jama'ar Sin da na Afirka, ta hanyar yin azama kan ka'idojin tuntubar juna, da bayar da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna. Yayin da dandalin ke cika shekaru 25 da kafuwa a shekara mai zuwa, ya zama wani muhimmin dandali na tattaunawa tare da samar da ingantacciyar hanyar yin hadin gwiwa a aikace tsakanin Sin da Afirka, wanda aka gina bisa tushen sada zumunci, da mutuntawa, da amincewa, da samun moriyar juna.

Dangantakar da ke tsakanin kasashen Afirka da Sin ta dogara ne kan mutunta juna, da daidaito, da hadin gwiwar samun nasara tare. FOCAC ya samar da kafar ganawa ga kasashen Afirka da kasar Sin don yin musayar ra'ayi, da kulla yarjejeniyoyin, da samar da dabarun karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da bunkasa ci gaban Afirka mai dorewa. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)