logo

HAUSA

Li Haili Tana Matukar Son Nau’o’in Kayan Marmari Daga Afirka

2024-08-21 20:36:41 CMG Hausa

Bayan da aka kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000, an samu karuwar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka, kuma an ci gaba da fadada fannonin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Ba ma kawai hadin gwiwarsu ya sa kaimi ga bunkasuwar Sin da Afirka baki daya ba, har yana canza rayuwar jam’ar Sin da Afirka. A halin yanzu, ko a kasar Sin ko a Afirka, ana ci gaba da bayyana irin wadannan labaru. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji labarai guda uku, mu ga yadda hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya kawo alheri ga al'ummar Sin da Afirka.