logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin da zai lura da aiwatar da umarnin kotun kolin Najeriya a kan ’yancin gashin kan kananan hukumomi

2024-08-21 09:35:57 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da kwamitin ma’aikatu mai wakilai 10 da zai tabbatar da yin aiki da hukuncin kotun kolin kasar da ya baiwa majalissun kananan hukumomi damar cin gashin kansu.

Sakataren gwamnatin tarayya Mr Geoge Akume ne ya kaddamar da kwamitin jiya Talata 20 ga wata a ofishinsa dake Abuja. Ya ce, kafa kwamitin ya zo daidai da kudurin gwamnatin tarayya wajen ganin cewa kananan hukumomin kasa guda 774 suna tafiyar da ayyukansu kamar gwamnatocin jihohi da na tarayya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Tun dai a ranar 11 ga watan Julin da ya gabata ne dai kotun kolin ta zartar da hukunci a kan dokar ’yancin kananan hukumomi wanda ya kawo karshen takaddama tsakanin gwamnonin kasar da kuma gwamnatin tarayya.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya ce lokaci ya yi da ya kamata majalissun kananan hukumomi su rinka gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan din gwamnoni ba domin dai samun ci gaban yankunan karkara cikin hanzari.

Sanata George Akume ya ce, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya damu matuka wajen ganin cewa ana amfani da sashen dokar da ta baiwa kananan hukumomi cikakken ’yancin da ya kamace su.

Muhimmi dai daga cikin aikin ’yan kwamitin shi ne tabbatar da ganin kananan hukumomi suna samun kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya tare kuma da amfani da kudaden wajen kyautata rayuwar mazauna karkara ba tare da sanya bakin gwamnatocin jihohi ba, kamar dai yadda hukuncin kotun kolin ya zayyana.

Mambobin kwamitin sun hada da sakataren gwamnatin tarayya wanda zai kasance shugaba, sauran su ne ministan kudi na kasar da ministan shari’a da kuma akanta-janaral na tarayya da gwamnan babban bankin kasa na CBN da shugaban hukumar rabon arzikin kasa, sai kuma wakilan gwamnoni da na kananan hukumomi. (Garba Abdullahi Bagwai )