Sin ta gudanar da ayyukan tallafin zaman rayuwar jama'a a nahiyar Afirka
2024-08-21 10:50:00 CMG Hausa
A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a jiya, jami’in hukumar kula da hadin gwiwa da samun bunkasuwa tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin ya yi bayanin cewa, tun daga shekarar 2021, Sin ta gudanar da ayyukan tallafin zaman rayuwar jama’a a nahiyar Afirka da dama, an riga an kiyaye guda hudu a cikinsu a nahiyar Afirka.
Bisa bayanin da aka yi, wadannan ayyukan hudu sun hada da samar da shinkafar da aka tagwaita, da maganin zazzabin cizon sauro na Artemisinin, da fasahohin shuke-shuken Juncao, da kuma horar da kwararru. A sakamakon hakan, an taimakawa kasashen da abin ya shafa da damar samun karin yawan shinkafa da suke nomawa daga tan 2 zuwa tan 7.5 a kowane hekta, kana an rage yawan mutane masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kashi 98 cikin dari.
Haka zalika kuma, Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen inganta karfinsu na shuka hatsi da kansu ta hanyoyin kafa cibiyar fasahohin aikin noma, da tura masanan aikin noma, da nuna goyon baya ga kamfanonin Sin, na yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka da sauransu. (Zainab Zhang)