An bude taron mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2024 a birnin Beijing
2024-08-21 11:29:53 CMG Hausa
A yau Laraba ne aka bude taron mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2024 a birnin Beijing, taron da zai gudana tsawon yini 5 bisa jigon “Inganta sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko don more makoma ta zamani tare”, inda aka gudanar da taron dandalin tattaunawa, da bikin baje koli, da gasanni da bukukuwan da abun ya shafa.
Don gwada sabbin fasahohi da amfaninsu, kamfanoni 169 za su gwada kayayyakin kirkire-kirkire fiye da 600, wadanda fiye da 60 daga cikinsu su ne karo na farko aka gwada su a fili.
Kana za a gudanar da taron dandalin tattaunawa na kwanaki 3, da tattaunawa game da batutuwa masu alaka da hakan har karo 26, inda masana na cikin gida da na waje, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da ‘yan kasuwa da yawansu ya kai 416 za su tattauna kan sha’anin mutum-mutumin inji. (Zainab Zhang)