Mutane 50 suka mutu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Zixing dake tsakiyar Sin
2024-08-20 10:36:32 CMG Hausa
Hukumomin birnin Zixing a jiya Litinin sun tabbatar da mutuwar mutane 50, yayin da wasu 15 suka bace sakamakon sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya tun karshen watan Yuli a birnin da ke larding Hunan na kasar Sin.
Ruwan sama da ba a taba ganin irinta ba wadda ta biyo bayan guguwar iska ta Gaemi ta ruguza gidaje sama da 1,700 tare da haddasa zaftarewar kasa sau 65,000 a birnin Zixing.
Jami’ai sun ce an yi gaggawar kwashe mutane 23,419 zuwa mafaka sakamakon barnar ruwan sama mai karfin gaske a birnin.
Ya zuwa yanzu, an gyara hanyoyin mota, wutar lantarki, sadarwa da ruwan sha a dukkan yankunan da lamarin ya shafa a Zixing, kuma ana ci gaba da aikin ba da agajin gaggawa, a cewar hukumomi. (Yahaya)