logo

HAUSA

Philippines ta zamo mai tada zaune tsaye a yankin tekun kudancin Sin

2024-08-20 11:13:18 CMG Hausa

 

Jiragen ruwan dakarun tsaron teku biyu na Philipphines sun kutsa kai cikin yankin teku dake dab da tudun ruwa na Xianbin dake tsibiran Nansha na kasar Sin ba bisa izini daga gwamnatin kasar Sin ba a safiyar jiya Litinin.

Bidiyon da aka dauka a wurin ya nuna yadda wadannan jiragen teku suka yi biris da gargadin da bangaren Sin ya yi musu, inda suka yi karo da jirgin ruwan rundunar tsaron teku ta kasar Sin ko CCG, wanda ke gudanar da ayyukansa yadda ya kamata a wurin, da gangan bisa mataki mai hadari.

Rundunar CCG ta dauki matakan da suka wajaba bisa dokar cikin gida da ta kasa da kasa, kuma matakai sun dace da halin da ake ciki, daidai da kundin dokoki da nuna iyakacin hakuri.

Wannan ba shi ne karon farko da Philippines ta keta ikon Sin na mallakar yankunanta ba, tare da cin amanar alkawarin da ta yi, matakin da ya rage mutuncinta a duniya.

Tun daga karshen watan Yuni, Philipphines ta yi ikirarin cewa, za ta kara ma’ammala da Sin a bangaren harkokin diplomasiyya da CCG, don kiyaye kwanciyar hankalin sararin teku bisa hadin kai, amma a wani bangare na daban, ta dauki matakai masu hadari don ta da rikici a tekun kudancin Sin, ta dogaro da karfin ketare don shisshigi cikin harkokin wannan yanki.

Matakin da Philippines ta dauka ba keta sanarwar bangarorin daban daban a tekun kudancin Sin kadai ya yi ba, har ma ya keta matsayin kungiyar ASEAN a harkokin shiyya-shiyya, da ma keta muradun sauran kasashen ASEAN. Kuma ba shakka Philippines ta zamo mai kawowa ASEAN hadari da keta zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Amina Xu)