logo

HAUSA

Bikin inabi a Turfan

2024-08-20 16:41:08 CMG Hausa


Bikin inabi ke nan da aka gudanar a birnin Turfan na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Wannan biki ya karbi bakuncin jama’a da dama daga gida da waje don su dandana inabi da sauran kayayyakin da aka samar daga gare shi.

Turfan ya shahara da inabin da ake samarwa a wurin. A Turfan, akwai gonakin noman inabi mafiya fadi a kasar Sin, kuma nau’o’in inabi da ake samarwa a wurin ya kai 550. An kuma kafa wani cikakken tsari na noman inabi, da samar da busasshen inabi, da ma sauran kayayyakin da ake samarwa daga gare shi, da kuma fannin yawon shakatawa mai nasaba da inabi a wurin.