logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Vietnam

2024-08-20 09:34:36 CMG Hausa

A jiya Litinin ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam, kuma shugaban kasar Vietnam To Lam, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.

Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar Vietnam da muhimmanci a harkokin diflomasiyyarta, kuma Sin a shirye take ta ciyar da abotarsu mai dadadden tarihi gaba, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna, da cimma burin samun amincewar juna ta fuskar siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a aikace, da karfafa goyon bayan jama’a, da kara hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, da kyautata warware bambance-bambance.

A nasa bangare, To Lam ya ce, a ko da yaushe Vietnam ta dauki dangantakarta da kasar Sin a matsayin zabi mai muhimmanci da fifiko a manufofinta na ketare, kuma Vietnam na tsayawa tsayin daka kan ka’idar Sin daya tak.

Ya kara da cewa, kasarsa na son yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen karfafa mu'amala a dukkan matakai, da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin cinikayya, zuba jari, sufuri, yawon bude ido, da ilimi, don inganta gina al'ummar Vietnam da Sin mai makomar bai daya wanda ke dauke da muhimman tsare-tsare. (Yahaya)