Ministan harkokin wajen Rasha: Amurka ta amince a kai hari kan bututun jigilar gas na Nord Stream
2024-08-20 11:45:52 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov, ya ce tabbas wadanda suka kai hari kan bututun jigilar iskar gas na Nord Stream, sun samu amincewa daga gwamnatin Amurka, saboda sai da taimakonta ne kadai za a iya gudanar da wannan danyen aiki.
Sergey Lavrov, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da ya zanta da jaridar Izvestia. Ya ce bisa labarin da kafofin yada labarai na kasar Jamus suka bayar, an ce, wasu ’yan Ukraine na da hannu cikin lamarin, amma ba za su iya aikata laifin su kadai ba.
Jami’in ya kuma jadadda cewa, dole ne Jamus ta amsa duk wata tambaya game da aukuwar lamarin, domin kuwa Rasha za ta ci gaba da yi bincike a fili tsakanin kasa da kasa. (Amina Xu)