logo

HAUSA

Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afrika ta kai wani sabon matsayi

2024-08-20 19:26:04 CMG Hausa

An bayyana hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, a matsayin wanda ke ci gaba da kaiwa sabon matsayi tun bayan taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika na shekarar 2021, lamarin da ya samar da dimbin alfanu ga al’ummun bangarorin biyu.

Mataimakin ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin, Tang Wenhong ne ya bayyana haka, inda ya ce, karkashin shirye-shiryen dake mayar da hankali ga inganta cinikayya da zuba jari da rage talauci da raya aikin gona, hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da Afrika na samun ci gaba, inda Sin ta shafe shekaru 15 a jere, tana rike da matsayin babbar abokiyar cinikayya ta kasashen Afrika.

Ya kara da cewa, cikin shekaru 3 da suka gabata, an aiwatar da jerin ayyukan hadin gwiwa kamar tashar jiragen ruwa ta Lekki a kasar Nijeriya da babban titin Nairobi a kasar Kenya. Haka kuma, kasar Sin ta kuma tura masana aikin gona sama da 500 zuwa nahiyar domin horar da masana ayyukan gona kusan 9,000 a nahiyar, wanda ya samar da goyon baya mai karfi ga tsarin zamanantar da aikin gona a nahiyar Afrika.

A cewarsa, karkashin shirye-shiryen raya muhalli da kirkire-kirkiren fasahohi da sauransu, kamfanonin kasar Sin sun aiwatar da ayyuka da dama da suka jibanci amfani da makamashi mai tsafta a nahiyar Afrika, yayin da batiran lithium da kayayyaki masu nasaba da yin amfani da hasken rana da aka fitar zuwa Afrika suka karu sosai. (Fa’iza Mustapha)