logo

HAUSA

Adadin masu shigowa da fita daga kasar Sin ya karu a watanni 7 na farkon bana

2024-08-19 13:42:36 CMG Hausa

A yau Litinin ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da jerin tarukan manema labarai masu nasaba da jigon "Ingiza ci gaba mai inganci". A cewar ofishin, tsakanin watan Janairu da Yulin bana, adadin mutanen da suka yi shige da fice ta tashoshin shigowa kasar Sin sun kai miliyan 341, adadin da ya karu da kaso 62.34 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara, kana adadin ababen hawa da aka yi shige da fice ta jiragen ruwa, da na kasa, da masu bin hanyar mota cikin wannan wa’adi sun kai miliyan 18.176, karuwar da ta kai ta kaso 52.09 bisa dari kan na makamancin lokaci na shekarar bara.

A cewar wani jami’in hukumar lura da shige da fice ta kasar, ci gaban da aka samu a watannin 7, na da nasaba da managartan manufofi da matakan da ake aiwatarwa.

Jami’in ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru bisa daidaito, wajen ingiza matakan bude kofa a tsarin ayyukan shige da fice, da tallafawa jami’an kamfanonin sarrafa hajoji na kasar Sin da damammakin fita ketare, da baiwa kamfanonin waje damar shigo da na su hajojin kasar Sin, kana za a kara kyautata dukkanin matakan ingiza samar da ci gaba mai inganci.  (Saminu Alhassan)