logo

HAUSA

Jirgin ruwan dakarun tsaron teku na Philippine ya kutsa tsibirin Ren'ai Jiao ba bisa ka’ida ba

2024-08-19 10:20:59 CMG Hausa

Da misalin karfe 6 na sanyin safiyar Litinin din nan ne wani jirgin ruwan dakarun tsaron teku na kasar Philippine, ya yi kutse cikin tsibirin Ren'ai Jiao, duk kuwa da gargadi da bangaren dakarun tsaron teku na Sin ya yi masa.

A cewar rundunar tsaron teku ta Sin ko CCG, jirgin ruwan na Philippine ya yi watsi da gargadin da aka yi masa, tare da ci gaba da kutsawa tsibirin na Ren'ai Jiao, har ta kai ya yi karo da jirgin dakarun tsaron tekun Sin dake aikin sintiri.

Da yake karin haske game da lamarin, kakakin rundunar CCG Gan Yu, ya ce bangaren Philippine ne zai dauki alhakin aukuwar wannan lamari. Gan ya kara da cewa, matakin Philippine na maimaita takalar bangaren Sin ya haifar da mummunan yanayi na keta ikon mulkin yankunan Sin, ya kuma illata yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Don haka ya yi kira ga Philippine da ta gaggauta dakatar da aikata irin wannan takala, in ba haka ba ta shirya daukar alhakin duk wani mummunan yanayi da ka iya biyo baya. (Saminu Alhassan)