logo

HAUSA

Jami’in Iran: Sin da Rasha sun fi muhimmanci

2024-08-19 14:17:18 CMG Hausa

Abbas Araghchi, wanda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya zaba a nada a matsayin ministan harkokin wajen kasar ya bayyana muhimman manufofin harkokin wajen sabuwar gwamnatin kasar a jiya Lahadi, yana mai jaddada muhimmancin kasashen Sin da Rasha.

Ya kuma kara da cewa, kasashen Sin, Rasha da kasashen da suka goyi bayan Iran lokacin da take cikin takunkumi da kuma kasashe masu tasowa a Afirka, da Latin Amurka da kuma gabashin Asiya, za su kasance jigon manufofin harkokin waje na gwamnatin kasar. Araghchi ya ce ya kuma kuduri aniyar karfafa alaka da kasashen da ke makwabtaka da Iran da kuma hada ababen more rayuwa da nasu.

Dangane da nahiyar Turai kuwa, ya bayyana cewa, kyautata alaka za ta dogara ne ga Turai ta gyara matsayinta na rashin gaskiya da nuna kyama ga Iran.

Dangane da dangantaka da Amurka kuwa, Araghchi ya jaddada dabarun sarrafa rashin jituwa yayin da ake kokarin rage takunkumi. (Yahaya)