Hukumar MDD: Na'urorin likitanci na Sin na da inganci
2024-08-19 07:36:22 CGTN Hausa
A kwanan baya a wannan watan Agusta, tawagar aikin jinya ta rundunar sojin kasar Sin karo na 14 wadda ke tabbatar da zaman lafiya a yankin Wau na kasar Sudan ta kudu a madadin MDD, ta ci nasarar cin jarrabawar da hukumar MDD ta shirya mata kan ingancin na’urorin likitanci da kwarewarsu na ceton masu jin rauni da makamai da alburusai da motoci da sauran kayayyakin aiki da ake bukata. (Sanusi Chen)