logo

HAUSA

Hamas ta soki sabuwar shawarar tsagaita bude wuta a Gaza

2024-08-19 10:38:50 CMG Hausa

Hamas ta soki sabuwar shawarar tsagaita bude wuta a zirin Gaza da aka gabatar a makon jiya, da cewar tana fifita sharuddan firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, musamman kin amincewa da tsagaita bude wuta na dindindin.

Kungiyar ta ce shawarar ta yi daidai da bukatun Netanyahu da suka hada da kin amincewa da tsagaita bude wuta na dindindin, da mallakar hanyar Netzarim, da mashigar Rafah, da hanyar Philadelphi, da kuma kafa sabbin sharudda kan musayar fursunoni, lamarin da Hamas ta ce ya kawo cikas ga yarjejeniyar.

A ranakun Alhamis da Juma’a ne a birnin Doha, aka gudanar da wani sabon zagaye na shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda masu shiga tsakani uku suka fitar da sanarwar hadin gwiwa kuma suka bayyana cewa, an samu ci gaba mai ma’ana a tattaunawar, kuma bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da kokarinsu a cikin kwanaki masu zuwa don tattaunawa kan cikakkun bayanai game da aiwatar da yarjejeniyar.

A daya bangare kuma, ofishin Netanyahu ya nuna godiya ga kokarin masu shiga tsakani, kuma yana fatan za su jagoranci Hamas ta amince da sharuddan shawarar da aka gabatar a karshen watan Mayu.

Sai dai, Hamas, wacce ba ta shiga tattaunawar kai tsaye ba, ta zargi Isra'ila da kara sabbin sharudda a kan shawarar da aka amince da ita a baya, ta kuma zargi gwamnatin Amurka da kokarin haifar da "yanayi mai kyau amma na karya", tare da nuna shakku kan sakamakon shawarwarin. (Yahaya)