logo

HAUSA

Xu Lingna: ‘yar kasar Singapore dake dukufa wajen taimaka wa baki don jin dadin zamansu a kasar Sin

2024-08-19 21:28:15 CMG Hausa


Xu Lingna, wadda tsohon sunanta shi ne Linda Painan, 'yar kasar Singapore ce, ta shafe shekaru 27 tana zama a Shanghai. Ta lashe lambar yabo ta azurfa ta furen Magnolia ta Shanghai ta shekarar 2023. Gwamnatin birnin Shanghai ce ta kaddamar da wannan lambar yabon, wadda aka sanya wa sunan furen birnin wato furen Magnolia a shekarar 1989, domin karrama fitattun baki 'yan kasashen waje saboda kyakkyawar gudummawar da suka bayar wajen yin cudanyar kasa da kasa da birnin Shanghai.

Painan ita ce shugabar cibiyar baki ta TEC a karkashin Cibiyar Hidimar Rayuwa ta Iyali ta Shanghai. Manufar TEC ita ce a taimaka wa ‘yan kasashen waje wajen kyautata zaman rayuwa a kasar waje. Tare da goyon bayan gwamnatin yankin Changning da ofishin reshen Hongqiao na yankin, Painan ta kafa wani dandali na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jama'a, da aikin ba da hidima kai tsaye don taimakawa 'yan kasashen waje da Sinawa da suka dawo daga kasashen waje su kara cudanya da zaman gida.

A karkashin jagorancin Painan, TEC ta shirya baje kolin kasa da kasa na 3E wato Kasuwanci, Samar da Aiki, da Masana’anta na tsawon shekaru hudu a jere tun daga shekarar 2020. Baje kolin ya kasance wani dandalin da ya hada kan kamfanoni na kasa da kasa da na cikin gida a birnin Shanghai, don samar da guraben ayyukan yi ga dubban mutane.  

Musamman ma, baje kolin yana taimaka wa masu neman aiki, wadanda suka samu aikin da ya dace, su kula da batun haraji, biza da sauran batutuwan da suka shafi aiki a wurin kai tsaye a teburin bayanai. Sakamakon haka, baje kolin yana taimakawa wajen daidaita tsarin daukar ma'aikata, kuma yana ba da hidimomi ga masu neman aiki. Ya zuwa yanzu, baje kolin ya samar da guraben ayyukan yi sama da 1,200, kuma ya jawo masu neman aiki yi sama da 5,000.

Bugu da kari, TEC tana ba da hidima na shawarwari akai-akai ga mutanen da ke neman takardar izinin aiki a kasar Sin. Ta gayyaci wakilan ma’aikatun gwamnati da su ba da laccoci kan manufofin haraji da shawarwarin doka da suka shafi kasashen waje kowace shekara. Irin wadannan abubuwan sun amfana wa mutane fiye da 50,000.

TEC ta kuma yi hadin gwiwa da kusan cibiyoyi 80, don shirya laccoci na walwalar jama'a da darussa masu jigo kan jagorar manufofi, musayar harsuna da al'adu, batutuwan kiwon lafiya, dokokin kasashen waje da ilimin yara.  

Painan ta bayyana cewa, "mun kuma shirya ayyukan musayar al'adu da hidimar jama'a, kuma mun tattara kudade ga gidajen reno da wuraren jin dadin yara. Tare da goyon bayan ofishin hadin gwiwa da musaya na gwamnatin yankin Changning da ofishin reshen Hongqiao, mun jagoranci malamai da kungiyoyin sa kai na Shanghai zuwa gundumar Liuchun da yankin Honghe na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, don gabatar da kwasa-kwasai kan ilimin halayen kwarai da kwasa-kwasan iyaye da yara ga yara da iyayen gida."

Painan ta kara da cewa, "A yayin bikin ranar mata ta duniya ta bana, mun dauki nauyin gudanar da wani taro kan jagorancin mata da harkokin kasuwanci. Burinmu ba wai kawai inganta karfin mata ba, har ma da samar da kudade don taimakawa mata da dama da ke da bukatar jinya da kuma samar da magunguna da tallafin ilimi, don samar musu da karin damammaki na yin fice a rayuwa."

Bayan ayyukanta a TEC, Painan ta saka ayyukan jin kai cikin rayuwarta ta yau da kullun. Tana gudanar da aikin tallafi, wanda ta hanyarsa take tallafawa yara, a yankunan tsaunuka na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta yadda za su kammala karatunsu.

Yunkurin da ta yi ya baiwa yara sama da 80 damar kammala karatunsu. Painan ta ce, "Ina yawan samun wasikun godiya daga wadannan yaran. Suna masu cewa, saboda taimakonmu, za su iya ci gaba da karatunsu, har ma da canza yanayin rayuwarsu, ina jin dadi da alfahari sosai."

A lokacin barkewar cutar COVID-19, Painan ta yi amfani da kudin Sin Yuan 830,000 kwatankwacin dalar Amurka 116,901 na kudin shigarta don sayan kayayyakin kariya, kuma ta ba da gudummawar wadannan kayayyakin ga wurare fiye da 70 a Shanghai. Ta kuma hada baki ma’aikata don kafa wata cibiyar sadarwa ta harshen Turanci, wacce ke ba da bayanai kan manufofin da suka dace da kuma kare kai.

Haka kuma tana saka ‘ya’yanta yin ayyukan agaji. Alal misali, ta kai babban danta zuwa wani yanki mai tsaunuka, a lardin Sichuan, don taimakawa wata makaranta gina hasumiya ta ruwa. A yayin bikin cikar karamin danta shekara daya da na biyu, ta kwadaitar da bakin da suka zo bikin da su ba da gudummawar kudi don taimakawa yara mabukata a Yunnan, wadanda ke bukatar tiyatar cututtukan zuciya, maimakon saya wa danta kyauta. Kudaden da aka tara a lokacin wadannan bukukuwan biyu sun taimaka wa yara da dama.  

Painan ta shaida yadda ake samun ci gaba a Shanghai a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ta ce, "An samu manyan sauye-sauye a fannin ci gaban bil Adama, kimiyya da fasaha, da tattalin arziki, da tsarin zamantakewa. Fahimtar mabambantan al'adu a Shanghai ya karu, kuma al'adun birnin sun kara kyau sosai. "

Idan aka zo maganar yanayin bunkasuwar Shanghai, Painan tana da nata hangen nesa game da TEC, ta ce, "Ina fatan TEC za ta zama wani dandali mai tasiri, wanda ba wai kawai yana ba da tallafi ga 'yan kasashen waje a Shanghai ba, har ma da inganta mu'amalar al'adu da cudanya da jama'a.  Daya daga cikin manufarta shi ne fadada ayyukan ba da tallafi, musamman wadanda suka shafi ilimi.”

Painan ta kuma yi fatan matan TEC za su kara himma, kuma za su yi musayar ra'ayoyinsu da tsara ayyuka masu ma'ana. Ta kara da cewa, "Mata su ne jigon kowane iyali. Idan Jigon ya kyautata, to iyali ya kyautata."

A farkon shekarar 2024, TEC ta zama kungiya mai zaman kanta ta farko a kasar Sin da ta samar da ayyukan ba da hidima ga walwalar jama'a da jin dadi kan dandalin labarai na birnin na CNS. CNS din, wani dandali ne na baki ma’aikata da ke neman bayanai a hukumance da hidimomin birane a Shanghai da kasar Sin. "Ina fata hakan zai ba wa dimbin jama'ar baki damar samun bayanai da tallafin da suke bukata cikin sauki," in ji Painan.(Kande Gao)