logo

HAUSA

An gudanar da bikin kunna fitilu na Xiaoliangshan karo na 8 a gundumar Mabian

2024-08-19 20:35:38 CMG Hausa

An gudanar da bikin kunna fitilu na Xiaoliangshan karo na 8 a gundumar Mabian ta kabilar Yi, mai cin gashin kanta dake lardin Sichuan, jiya Lahadi da dare. Yayin bikin an kunna fitilu masu dimbin yawa da suka kayatar da jama’a har ma da masu yawon bude ido daga fadin duniya, lamarin da ya nuna kyawun al’adun kabilar Yi na musamman.

A wajen bikin, dukkan mutanen da suka zagaye wutan da aka kunna, rike da hannun juna, sun taka rawar Da Ti ta kabilar Yi cike da farin ciki. Masu rawan, sanye da kyawawan tufafi da kayayyakin ado na kabilar Yi, sun taka rawa dake nuna kuzari da farin ciki na al’ummar Yi.

Bikin, daya ne daga cikin manya manyan bukukuwan al’dun gargajiya na al’ummar Yi. Yana da daddaden tarihi, kana muhimmiyar al’ada ce da aka gada daga zuri’a zuwa zuri’a.(Fa'iza Mustapha)