logo

HAUSA

Li Qiang zai kai ziyarar aiki a kasar Rasha

2024-08-19 15:30:07 CMG Hausa

Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar da cewa, bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Vladimirovich Mishustin, da firaministan kasar Belarus Roman Golovchenko suka yi masa, firaministan kasar Sin Li Qiang zai kai ziyarar aiki a kasashen biyu, da kuma jagorantar taron ganawar firaministocin Sin da Rasha karo na 29, a tsakanin ranakun 20 zuwa 23 ga watan Agusta. (Maryam Yang)