logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta jinkirta shirinta na bayar da rance ga masu kanana da matsakaitan masana’antu zuwa watan gobe

2024-08-19 09:21:16 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da dage shirinta na bayar da rance ga masu kananan da matsakaitan masana’antu zuwa watan gobe.

Ministar masana’antu, kasuwanci da harkokin zuba jari Dr. Doris Uzoka-Anite ce ta sanar da hakan jiya Lahadi 18 ga wata a Calabar ta jihar Cross-Rivers lokacin da ta gana da mutanen da suka amfana da shirin tallafin kudi na shugaban kasa da kuma masu kananan masana’antu da suke dakon fara amfana da shirin rancen kudi daga gwamnatin tarayya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministar ta ce, ya zuwa yanzu masu kananan sana’o’i dubu dari shidda da sittin da dari uku da ashirin ne daga cikin mutane miliyan daya a kananan hukumomin Najeriya 774  suka amfana da tallafin kudi karkashin shirin tallafawa masu kananan sana’o’i da jari.

Amma dai ministar ta ce, gwamnati ta kara tsawaita lokacin da za ta fara bayar da rancen kudi ga kanana da matsakaita masu masana’antu, inda yanzu za a fara aiwatar da shirin ne a watan gobe.

Ta ce dai, a zancen nan da ake yi adadin mutane dubu dari bakwai ne suka nuna bukatar samun wannan rance.

Ministar ta ce, domin tabbatar da adalci wajen bayar da rance, ta bukaci shugabanni da kungiyoyin al’umma da su shigo cikin shirin ta hanyar sanya idanu wajen aiwatar da shi.

Shi dai wannan shirin rance mara ruwa da shugaban kasa ya bullo da shi, an kebe masa tsabar kudi naira biliyan dari 2 ne, a inda za a rabar da naira biliyan 125 ga kanana da matsakaita masana’antu, yayin da kuma raguwar zai tafi ga masu manyan masana’antu, wanda wannan kamar yadda minister ta ce babu shakka zai buda kofofin ci gaban tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi domin dai samun kyakkyawar makoma ga kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)