logo

HAUSA

MDD ta yi maraba da matakin Sudan na sake bude iyakarta da Chadi domin shigar da kayayyakin agaji

2024-08-18 17:17:23 CMG Hausa

 

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yaba da matakin kasar Sudan na sake bude iyakar Adre dake tsakaninta da kasar Chadi, domin shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin Darfur da yaki ya daidaita.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar jiya, Antonio Guterres ya yaba da matakin yana mai bayyana hanyar a matsayin mafi sauki da za ta isar da kayayyakin agaji kai tsaye ga miliyoyin ‘yan Darfur dake cikin matsananciyar yunwa.

A ranar Alhamis ne gwamnatin rikon kwarya ta Sudan, ta yanke shawarar sake bude iyakar Adre dake tsallakawa zuwa Chadi na tsawon watanni 3, domin ba da damar isar da kayayyakin agaji ga mutanen da yakin dake wakana a kasar ya shafa. (Fa’iza Mustapha)