logo

HAUSA

Najeriya ta rage adadin wakilan ta da za su halarci babban taron majalissar dinkin duniya karo na 79 a watan gobe

2024-08-18 16:47:32 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin rage adadin yawan jami’an gwamnatin da za su halarci babban taron majalissar dinkin duniya da za a gudanar a watan gobe na Satumba.

Shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa Mr. Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan jiya Asabar 17 ga wata a madadin shugaban kasa, yayin taron karawa juna sani na yini guda da aka shiryawa shugabannin hukumomin dake karkashin kulawar ofishin shugaban kasa a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban ma’aikatan ya ce gwamnati ta yanke shawarar rage adadin wakilan ta a wajen taron karo na 79 da za a gudanar a hedkwatar majalissar dinkin duniyar dake birnin NewYork, a kokarin da ake yi domin rage adadin kudaden da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da harkokin ta da ba su da nasaba da ayyukan raya kasa.

Ya ce tun bayan zanga zangar da al’ummar kasa suka yi, gwamnati ta fara tattaunawa a kan yadda za ta rage yawan wadanda za su halarci taron daga Najeriya, inda ya ce a lokutan baya, Najeriya na kan gaba wajen daukar nauyin mutune masu yawa zuwa wajen taron, lamarin dake janwowa kasa asarar makudan kudade.

Shugaban ma’aikatan na fadar shugaban kasa, ya ci gaba da bayanin cewa gwamnati ta lura wasu daga cikin wakilan Najeriya na amfani da irin wadannan manyan tarukan duniya ne wajen samun damar gudanar da wasu harkokin gaban su.

A saboda haka yanzu duk wanda ba shi da wata gudummawa da zai bayar a wajen taron na watan gobe, shugaban kasa ya yi umurnin kada a ba shi damar zuwa.

Da yake magana kuma a kan taron karawa juna sanin, Mr. Femi Gbajabiamila ya ce na shirya taron ne domin kara ilimintar da jami’an nauye nauyen da ya rataya a wuyan su ta fuskar zartar da kudurori da suka shafi manufofin gwamnati da kuma wasu ka’idoji da za su tabbatar da gudanuwar ayyukan cikin nasara. (Garba Abdullahi Bagwai)