logo

HAUSA

Na’urar bincike ta karkashin teku ta kasar Sin ta kammala nutsu a karo na 300

2024-08-18 21:12:03 CMG Hausa

Na’urar bincike ta Jiaolong ta kasar Sin mai nutso karkashin teku ta kammla nutso a karo na 300 tun bayan wanda ta yi karon farko a watan Agustan shekarar 2009.

Na’urar Jiaolong dauke da masani kimiyya daya da matukanta biyu, ta yi nutso ne a yankin yammacin tekun Pasifik. Wannan kuma shi ne nutso na farko cikin 18 da aka tsara za ta yi yayin wani binciken kimiyya dake gudana.

Jirgin ruwan bincike na kasar Sin mai lamba 1 ne ya dauki. Haka kuma, jirgin na dauke da masana kimiyya na ciki da wajen kasar Sin, inda ya tashi daga Qingdao dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin a ranar 10 ga wata.

Yayin aikin binciken na kwanaki 45 a yammacin tekun Pasifik, an tsara na’urar Jiaolong za ta tattaro wasu halittun dake karkashin teku da ruwan teku da duwatsu, lamarin dake da nufin fadada fahimtar dan Adam kan irin muhallin halittu da na tuddan teku. (Fa’iza Mustapha)