'Yan bindiga sun yi garkuwa da sama da dalibai 20 da suke nazarin koyon aikin likitanci a jihar Benue
2024-08-17 10:52:09 CMG Hausa
Sama da dalubai 20 da suke nazarin aikin likita yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue dake arewa ta tsakiyar Najeriya.
Al`amarin ya faru ne da yammacin ranar alhamis 15 ga wata a daidai garin Otukpo lokacin da daliban ke kan hanyar su ta zuwa Enugu domin halartar babban taron kungiyar dalibai masu nazarin cutukan da suka shafi hakora ta kasa.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Daluban da wannan al`amari ya shafa sun fito ne daga jami`ar Maiduguri da kuma ta garin Jos, kamar dai yadda jami`ar hulda da jama`a ta rundunar `yan sandan jihar Benue SP Catherine Anene ta shaidawa manema labarai.
SP Catherine ta ce rundunar ta samu labarin yin garkuwar da daluban ne mintina kalilan da afkuwar al`amari ta hannun wata daluba data kira waya inda take bayyana cewa ita daluba ce dake karatu a jami`ar Jos, kuma yar uwarta ta turo mata da sako na karta ta kwana cewa sun fada hannun `yan bindiga kuma sun dauke su zuwa wani waje na daban .
“Wani lokaci can a watan da ya gabata, munyi gabatar da wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a wannan yanki, koda yake wasu daga cikin su sun tsare a lokacin da jami`an mu suka kai masu farmaki, muna kuma kyautata zaton wadanda suka tsaren ne sukayi garkuwa da wadannan dalubai”. (Garba Abdullahi Bagwai)