Jirgin ruwan Sin mai dauke da asibitin tafi da gidanka ya kammala aiki a Mozambique
2024-08-17 16:27:17 CMG Hausa
Jirgin ruwan kasar Sin mai dauke da asibitin tafi da gidanka, dake bayar da agajin jinya ga marasa lafiya a sassa daban daban na duniya wato Peace Ark, ya kammala aiki a kasar Mozambique a jiya Juma’a, inda kuma ya tashi daga gabar ruwan Maputo zuwa Afirka ta kudu, inda zai yada zango don gudanar da zango na 5 na ayyukan sa.
A yini 7 da ya shafe yana aiki a Mozambique, likitocin jirgin sun gudanar da ayyukan tiyata 74 ga marasa lafiya, wadanda suka hada da na aikin yanar ido da cire duwatsu, ya kuma samar da hidimomin lafiya ga sama da al’ummun wurin 7,300.
Kari kan hakan, wasu jami’ai dake cikin tawagar jirgin ruwan, sun ziyarci wasu asibitoci da sansanonin sojin kasar, inda suka duba marasa lafiya, tare da yi musu jinya, kana sun yi musayar ilimi da takwarorin su na Mozambique. (Saminu Alhassan)