Daliban Habasha sun sha alwashin inganta dangantakar dake tsakanin kasarsu da ta Sin
2024-08-16 11:20:09 CMG Hausa
Daliban jami’o’in kasar Habasha sama da 300 ne suka samu tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin don taimaka musu wajen yin karatun digiri da na gaba da digiri a fannonin ilimi daban-daban a manyan jami’o’in kasar Sin.
A ranar Alhamis ne aka gudanar da bikin bankwana da horo na musamman a ofishin jakadancin Sin dake kasar Habasha ga daliban na Habasha a gaban jami’an gwamnatin Habasha, da jami’an diflomasiyyar kasar Sin dake Habasha, da iyalan wadanda suka samu tallafin karatu.
Idossa Terfassa, shugaban ofishin bayar da tallafin karatu da harkokin kasa da kasa na ma'aikatar ilimi ta Habasha, ya jaddada muhimmancin karin tallafin karatu da kasar Sin ke bayarwa a matsayin wani bangare na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu wajen habaka kwarewa.
Terfassa ya kara da cewa, tallafin karatu na kasar Sin yana taka muhimmiyar rawa a matsayin kasa mai ba da taimako wajen ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma gaba, da bunkasa fasahohin zamani a kasa wadda ke gabashin Afirka. (Mohammed Yahaya)