Sin a shirye take ta wanzar da tattaunawa da dukkanin sassa don warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa
2024-08-16 20:30:06 CMG Hausa
A yau Juma’a mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, har kullum burin Sin shi ne yayata matakan wanzar da zaman lafiya da sulhu, kuma a shirye take ta wanzar da tattaunawa da dukkanin sassa, don samar da yanayin warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, bisa shawarwari da shiga tsakani.
Lin Jian, ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin da manema labarai na kasashe daban daban suka yi masa, yayin taron ‘yan jarida da aka saba gudanarwa.
Game da yadda jirgin ruwan dakarun tsaron teku na Philippine ke ci gaba da kasancewa a yankin tsibirin Xianbin ba bisa ka’ida ba kuwa, Lin Jian ya ce Xianbin yankin ruwa ne na tsibiran Nansha mallakin kasar Sin. Kuma jirgin ruwan Philippine din ya shiga yankin Xianbin ba tare da neman izini ba, ya kuma kasance a wurin tsawon lokaci, wanda hakan ya yi matukar keta ikon mulkin yankunan kasar Sin.
To sai dai kuma, kasar Sin ta gabatar da korafi mai karfi ga Philippines ta hanyoyin diflomasiyya da suka dace, tana mai bukatar Philippines din ta gaggauta janye jirgin ruwan na ta ba tare da wani bata lokaci ba. (Saminu Alhassan)