logo

HAUSA

Rundunar sojin Amurka ta shirya wata rawar daji ta “Bamboo Eagle”

2024-08-16 15:32:45 CGTN Hausa

Bisa labarin da shafin intanet na “The WarZone” na kasar Amurka ya bayar, an ce, a kwanakin baya, rundunar sojin Amurka ta shirya wata rawar daji ta “Bamboo Eagle”, inda ta sanya jirgin saman yaki samfurin J-20 da na H-20 na kasar Sin a matsayin abokan gaba. Ta kuma shigar da jiragen saman yaki samfurori iri daban daban, kamar F-22 da F-35 da F-16 da B-1B、B-52H da kuma E-3 da E-11da RC-135, yawansu gaba daya ya kai 150, ciki har da jiragen sama na kara mai guda 17 a fagen rawar daji. Kasashen Burtaniya da Australiya ma sun tura wasu jiragen saman yaki nasu yayin rawar dajin domin nuna wa bangaren Amurka goyon baya. (Sanusi Chen)