Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutane 50 a arewacin Chadi
2024-08-16 11:26:29 CMG Hausa
Hukumomi da kafafen yada labarai na kasar Chadi sun bayyana a jiya Alhamis cewa, a kalla mutane 54 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin Tibesti dake arewacin kasar Chadi.
Gwamnan lardin Tibesti Mahamat Tochi Chidi ya ce, ruwan saman da ta fara sauka tun daga ranar Juma'ar makon jiya har zuwa Laraba ta lalata kadarori. Yayin da kafafen yada labarai na cikin gida suka rawaito cewa sama da mutane 50,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a lardin.
Ministan kula da harkokin jin dadin jama'a, da hadin kan kasa da kuma harkokin jin kai na kasar, Fatime Boukar Kossei, ta fada a jiya Alhamis cewa, an kafa matsuguni na wucin gadi domin karbar 'yan gudun hijira.
Kasar Chadi dai na fuskantar ambaliyar ruwa tun tsakiyar watan Mayu wanda tuni ya shafi mutane 245,000, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya. (Mohammed Yahaya)