logo

HAUSA

Kusan yara miliyan 500 na shafe sama da rabin shekara cikin matsanancin yanayin zafi

2024-08-15 10:19:53 CMG Hausa

Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) ya ce kusan yara miliyan 500, galibinsu a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika, na shafe sama da rabin shekara cikin yanayin zafi da ya haura digiri 35.

Babbar daraktar asusun UNICEF Catherine Russel, ta ce yaran ba baligaggu ba ne. Jikinsu na da rauni ga yanayin zafi. Kuma jikin kananan yara yana daukar zafi cikin sauri, yayin ya kan dauki lokaci kafin zafin ya sauka. Ta ce matsanancin zafi ya fi hadari ga jarirai saboda yadda zuciyarsu ke bugawa da sauri, don haka karuwar zafi ya fi damun yara.

Ta ce yanzu kamar an riga an saba da raneku masu tsananin zafi. Tana cewa, tsanantar zafi na kawo tsaiko ga lafiyar yara da walwalarsu da harkokinsu na yau da kullum.

A cewarta, dole ne gwamnatoci su dauki matakan shawo kan karuwar yanayin zafi. Kuma UNICEF na kira ga shugabanni da gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu, da su gaggauta samarwa tare da daukar mataki kan yanayi, domin daukaka hakkin kowane yaro na samun muhalli mai aminci da tsafta kuma mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)