logo

HAUSA

WHO ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin batun lafiyar al’umma dake bukatar daukin gaggawa

2024-08-15 10:53:50 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin barazanar lafiyar al’umma dake bukatar daukin gaggawa a duniya, tana mai gargadin yiwuwar karuwar bazuwar cutar a duniya.

Kawo yanzu, adadin wadanda suka kamu da cutar kyandar biri ya zarce wanda aka samu a bara, inda yawansu ya kai sama da 14,000 tare da sanadin mutuwar 524.

Matakin na WHO na zuwa ne bayan cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika (Africa CDC), ta ayyana cutar a matsayin barazanar lafiyar al’umma dake bukatar daukin gaggawa a nahiyar.

Darakta janar na hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jawabinsa na bude wani taron gaggawa da hukumar ta kira jiya a Geneva cewa, tabbatar da barkewar cuta a matsayin mai bukatar daukin gaggawa a duniya, ka iya gaggauta kokarin bincike da samar da kudade da inganta matakan kula da lafiyar al’umma da hadin gwiwa, wadanda ke da muhimmanci wajen dakile cutar da hana karuwar bazuwarta. (Fa’iza Mustapha)