logo

HAUSA

Xi ya ce kasarsa a shirye take ta yi aiki tare da Brazil wajen ingiza gina al’ummar Sin da Brazil mai makomar bai daya

2024-08-15 18:39:36 CMG Hausa

A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa a shirye kasarsa take ta yi aiki kafada da kafada da Brazil, da nufin mayar da bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya dake tsakanin su wani sabon mafari, na hada karfi don gina al’umma mai makomar bai daya tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne cikin sakon taya murnar da ya aike ga takwaransa na Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, albarkacin bikin cikar kasashen biyu shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya.

A nasa sakon ga shugaba Xi Jinping kuwa, shugaba Lula da Silva, cewa ya yi alakar Brazil da Sin na kara zama wani jigo, na gina tsarin raba tasiri tsakanin sassan kasa da kasa, da kuma samar da tsarin gudanar da duniya mai inganci kuma bisa adalci. (Saminu Alhassan)