Ya kamata tuba daga laifin yaki da tsoffin sojojin Japan ke yi ya zama matsaya guda ta daukacin ‘yan siyasar Japan
2024-08-15 20:34:36 CMG Hausa
Shekaru 79 da suka wuce, daidai da ranar 15 ga watan Agustan nan, kasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da wani sharadi ba. Bayan shekaru 14 ana zubar da jini da sadaukarwa mai girma, al’ummun kasar Sin sun cimma babbar nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan.
To sai dai kuma duk da haka, da sanyin safiyar yau, ministan tsaron Japan da wasu tarin ‘yan siyasar kasar sun ziyarci haikalin Yasukuni, wurin da aka ajiye alluna masu dauke da sunayen manyan kusoshin kasar da suka aikata laifukan yaki yayin yakin duniya na II.
A daidai wannan lokaci ne kuma wani dattijo mai shekaru 94, dake cikin sojojin Japan din da suka yi wancan yaki karkashin runduna ta 731, fannin amfani da kwayoyin halittun bacteria domin yaki, mai suna Shimizu Hideo, ya ziyarci birnin Harbin inda ya amince da aikata laifi tare da neman afuwa.
Tabbas halayyar ‘yan siyasar Japan ta sabawa ta tsohon sojin kasar wanda ya waiwayi abubuwan da suka auku na munin laifukan yaki, kuma ko shakka babu lamarin na iya jefa sauran sassan duniya cikin damuwa, game da hadarin sake farfadowar akida mai hadari ta Japan ta amfani da karfin soji.
A cewar dattijo Shimizu Hideo, "Idan har ba a baiwa yara damar sanin ainihin abun da ya auku a tarihi ba, da irin mummunan sakamako da bala’in da yaki ya haifar, ko shakka babu Japan ba ta da makoma." Hideo ya kara da cewa, wannan tunani na waiwayen laifin da aka tafka a baya da neman afuwa, ya dace ya zama matsaya guda ta daukacin ‘yan siyasar Japan. (Saminu Alhassan)