logo

HAUSA

Gwamnan yankin Yamai ya dauki matakan yaki da barace-barace a birnin Yamai

2024-08-15 18:49:25 CMG Hausa

A yayin wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata 13 ga watan Augustan shekarar 2024, babban gwamnan yankin Yamai, birgadiye janar Abdou Assoumane Harouna ya sanar da cewa daukar matakai domin yaki da barace-barace a cikin birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ganin yadda bara take kamari a birnin Yamai ne, mun dauki niyyar magance matsalar ta hanyar kwararrun matakai, da suka hada da tattara da tura wadannan mabarata kauyukansu, idan har suka dawo da sunan bara to su kuka da kansu, in ji gwamnan birnin Yamai.

An baiwa jami’an tsaro na ’yan sanda da jandarma na kasancewa a muhimman wurare na birnin Yamai domin kwashe masu bara da mai da su garuruwansu. Hukumomin birnin Yamai sun hana barace-barace a wuraren jama’a.

Wannan bara na janyo matsaloli ga zaman rayuwar al’umma, musammun ma kan haduran da take hadasawa a kan hanyoyi.

A dunkule, bigadiye janar Abdou Assoumane Harouna ya bayyana cewa masu bara za’a kai su kebebbun wuraren noman gandari na Kandadji da ke yankin Tillabery da kuma wuraren noma gandari da ke yankin Diffa, domin gudanar da ayyukan noma a matsayin wani horo da ladabtawa.

A cewar gwamnan birnin Yamai, mutane sun maida bara tamkar wata sana’a ko wani aiki, wannan kuma halayya ce ta raggaye, a yayin da yawancin ’yan Nijar suke fadi ka tashin zuwa aiki domin  neman halaliyarsu tare da bada taimako ga ci gaban kasa, a yayin da wasu mutane suke cikin gonaki suna aiki, a lokacin nan ne wasu mutanen suke mika hannu domin yin bara, dare da rana basu da wani aiki ko sana’a sai barace-barace, to wannan ya kare, in ji gwamna Abdou Assoumane Harouna. (Mamane Ada)