logo

HAUSA

Sin na fatan Japan za ta yi taka tsantsan game da kalamai da ayyukan ta game da batutuwan tarihi

2024-08-15 21:16:21 CMG Hausa

A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi tsokaci game da ziyartar haikalin Yasukuni da wasu ‘yan siyasar Japan suka yi, wurin da aka ajiye alluna masu dauke da sunayen manyan kusoshin kasar da suka aikata laifukan yaki.

Lin Jian, ya ce matakin na wasu ‘yan siyasar Japan game da haikalin na Yasukuni ya sake nuna kuskuren Japan, game da wannan muhimmin batu na tarihi. Sin ta yi kira ga Japan da ta rungumi gaskiya, ta martaba sanarwa daban daban da ta fitar, da alkawuran da ta dauka don tunawa kai mummunan tasirin yakin nuna karfin tuwo da ta aiwatar, kana ta yi taka tsantsan wajen furta kalamai, ko aikata wasu matakai game da batun tarihi irin na haikalin Yasukuni. (Saminu Alhassan)