Ma’aikatar tsaro a tarayyar Najeriya ta ce sojojin kasar na bukatar alburusai miliyan 200 a duk shekara
2024-08-15 09:53:57 CMG Hausa
Karamin ministan tsaron Najeriya Alhaji Bello Matawalle yace dakarun sojin kasar suna bukatar a kalla adadin alburusai miliyan 200 a duk shekara wajen gudanar da aikin su.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 14 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ma’aikatar tsaro ta kasa da kamfanin samar da makamai na kasa DICON da kuma hukumar fasahar kere-kere ta Najeriya, a shirye-shiryen da ake yi na assasa kamfanin da zai mayar da hankali wajen samar da alburusai a Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan ya ce, gwamnati na kashe a kalla dala biyu wajen sayen kowanne alburushi guda daya, lamarin da ya bayyana da cewa abun kunya ne mutuka.
Alhaji Bello Matawalle ya ci gaba da bayanin cewa, adadin alburusai miliyan 200 iya sojoji ne kawai suke bukata, amma idan an hada da sauran hukumomin tsaro da ’yan sanda Najeriya na bukatar kusan alburusai miliyan 350 a duk shekara.
Haka kuma ministan ya sha alwashin cewa, kafin karewar wa’adin farko na shekaru hudun wannan gwamnati, za a tabbatar da ganin cewa kamfanin samar da kayayyakin tsaro na kasa wato DICON zai dawo da fitar da kayan da yake samarwa zuwa kasashen ketare kamar yadda aka san shi a baya.
“Muna da karfin da za mu iya samar da wadannan alburusai, kamar yadda kuna sani a baya kasashen Afrika da dama suna zuwa wannan kamfani na DICON domin sayen makamai.”(Garba Abdullahi Bagwai)