Tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata a watan Yuli
2024-08-15 16:09:37 CMG Hausa
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar a yau Alhamis sun shaida cewa, a watan Yulin bana, an ci gaba da farfado da bukatun samar da kayayyaki a kasar, kuma yadda ake samar da guraben aikin yi da kuma farashin kayayyaki suna kan wani mataki na daidaito, tattalin arziki kuma ya bunkasa yadda ya kamata. Duk da haka, ci gaban farfadowar tattalin arzikin na fuskantar dimbin matsaloli da kalubale, don haka, a mataki na gaba, za a bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko bisa yanayin da sassan kasar ke ciki, tare da mai da hankali a kan inganta bunkasuwar tattalin arziki, don kara inganta tushen farfadowar tattalin arzikin. (Lubabatu Lei)