logo

HAUSA

Sin na shirin amfani da fasahohin dijital wajen bunkasa magungunan gargajiya na kasar

2024-08-15 18:53:03 CMG Hausa

Hukumar dake lura da harkar magungunan gargajiya ta kasar ko NATCM, ta ce Sin na shirin samar da tsarin amfani da fasahohin dijital, wajen bunkasa cin gajiya daga magungunan gargajiya na kasar.

Hukumar ta ce shirin da ake fatan aiwatarwa cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa, zai bayar da damar hade fasahohin dijital da dabarun cin gajiya daga magungunan gargajiyar kasar ko TCM.

Ana sa ran karkashin tsarin za a yi amfani da fasahohi da suka hada da na manyan bayanai, da kirkirarriyar basira wajen raba bayanai game da gajiyar magungunan na TCM, da taimakawa wajen gina tsarin “dijital da TCM, bisa amfani da na’urori masu kwakwalwa”. (Saminu Alhassan)