logo

HAUSA

Shirin tsaftace ruwa na Sin ya lashe lambar karramawa ta kasa da kasa a fannin kirkire kirkire

2024-08-14 19:15:15 CMG Hausa

Kungiyar kasa da kasa mai rajin samar da ruwa mai inganci ko IWA, ta baiwa wani shirin tsaftace ruwa na kasar Sin lambar karramawa ta kasa da kasa a fannin kirkire kirkire.

Shirin na Sin mai lakabin "Zaburar da fasaha da sauya akalar kasuwa: tsarin Sin na cin gajiya daga dabarun tace ruwa" ya yi nasarar lashe lambar girmamawa ta IWA ne a bangaren managartar kirkire kirkire na shekarar 2024, yayin taron kasa da kasa na masu ruwa da tsaki game da albarkatun ruwa, da baje kolin fasahohi da ya gudana tsakanin ranakun Lahadi zuwa Alhamis din wannan mako a birnin Toronton kasar Canada.

Kungiyar IWA ta ce aikin na samar da dabarar jure kamfar ruwa tsakanin al’ummu a matakin farko, da taimakawa ayyukan noma ta hanyar samar da kasa mai kunshe da managartan sinadarai. Kaza lika, shirin ya zama wani misali na wanzar da salon kiyaye ingancin ruwa a dukkanin fadin duniya, wanda ke iya kara zaburar da wasu karin shirye shiryen, da hadin gwiwa tsakanin abokan tafiya na kasa da kasa a fannin. (Saminu Alhassan)