logo

HAUSA

Shugaban IOC ya aika sakon taya murnar nasarar kammala wasannin Olympics ga shugaban CMG

2024-08-14 10:38:53 CMG Hausa

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta duniya (IOC) Thomas Bach, ya aike da wasika ga shugaban babban rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin (CMG) Shen Haixiong, yana taya CMG murnar nasarar da aka samu wajen watsa wasannin Olympics na Paris tare da bayyana godiya ga dukkan ma’aikatan CMG da suka shiga aikin watsa wasanni.

Cikin wasikar mai kwanan wata 12 ga watan Augusta, Thomas Bach ya ce ba don goyon baya da jajircewar CMG ba, wasannin ba za su samu irin wannan gagarumar nasara ba. Ya kara da cewa, CMG ta taka muhimmiyar rawa yayin wasannin na Olympics na Paris da aka kammala cikin nasara.

Har ila yau, ya ce bisa goyon bayan CMG, an gabatar da kayataccen gasar wasannin Olympics ga masu kallo a fadin duniya. Yana mai cewa, IOC na bayyana godiya tare da alfahari da aiki da irin wadannan jajirtattun abokan hulda na kafafen yada labarai.

A cewar Bach, hadin gwiwar CMG da IOC ya nuna taken Olympic na “kara sauri da girma da karfi da karin hadin kai.”  (Fa’iza Mustapha)