Yankin Belgorod na kasar Rasha ya kafa dokar ta-baci a yankin mai fama da tashin hankali
2024-08-14 14:01:30 CMG Hausa
Gwamnan yankin Belgorod na kasar Rasha ya bayyana a shafinsa na Telegram a yau Laraba cewa, yankin Belgorod ya kafa dokar ta-baci a yankin saboda tabarbarewar al’amura, yayin da mahukunta ke tunanin daukaka yanayin na gaggawa zuwa matakin tarayya.
A cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, Gladkov ya ce, "Ana cikin mawuyacin hali da kuma tashin hankali a yankin Belgorod. Luguden wuta da sojojin Ukraine ke yi a kullum ya kai ga lalata gidaje, da kuma jikkata fararen hula, saboda haka, mun yanke shawarar kafa dokar ta-baci a duk fadin yankin Belgorod daga yau don samar da karin kariya ga jama’a da kuma ba da tallafi ga wadanda abin ya shafa”, a cewarsa.
Gwamnan ya kuma nuna cewa, nan ba da dadewa ba gwamnatin yankin za ta yi kira ga hukumar tarayya ta bukaci a kafa dokar ta-baci a matakin tarayya. (Mohammed Yahaya)