Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Ma’aikatan Sa Kai Masu Kula Da Muhalli A Yankin Tabkin Danjiangkou Na Lardin Hubei
2024-08-14 15:49:43 CMG Hausa
Albarkacin ranar kula da muhalli ta biyu ta kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping, ya amsa wasikar ma’aikatan sa kai masu aikin kare muhalli a yankin tabkin Danjiangkou dake Shiyan na lardin Hubei, yana mai karfafa musu gwiwa tare da aikewa da sakon gaisuwa ga dukkan ma’aikatan sa kai dake kare muhalli a fadin kasar.
Cikin wasikar, shugaba Xi ya ce “ina fatan za ku ci gaba da yayata ruhin aikin sa kai da bayar da gudunmuwa ga zamanantar da jituwa tsakanin dan Adam da sauran halittu.”
Cikin shekaru 10 da suka gabata, a matsayin muhimmiyar hanya ta tsakiya ta aikin karkatar da ruwa daga yankin kudu zuwa arewancin kasar Sin, al’ummun tabkin Danjiangkou da ma’aikatan sa kai a wurin, sun taimaka sosai ga aikin kula da kare ruwa. (Fa’iza Mustapha)