logo

HAUSA

Matasa Wadanda Aka Haifa Bayan Shekara ta 2000 Sun Zama Abin Alfahari Ga Kasa Da Iyayensu

2024-08-14 07:46:01 CGTN Hausa

Kasar Sin ta kammala gasar wasannin Olympics ta Paris ta 2024 da lambobin yabo 91 da suka hada da lambobin zinari 40, da lambobin azurfa 27, da tagulla 24. Wannan gagarumar nasarar ta ba su matsayi na biyu a gaba dayan adadin lambobin yabo kuma sun yi kunnen doki da Amurka wajen samun lambobin zinari mafi yawa a tsakanin kwamitin wasannin Olympics na kasa wato NOC, wanda ya zama karo na farko a tarihin Olympics na lokacin zafi da kasashe biyu suka yi kunnen doki a matsayi na farko a yawan lambobin zinari. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta zama kasa daya tilo, baya ga Amurka da tsohuwar Tarayyar Soviet, a kan yawan lambobin zinari a gasar Olympics ta lokacin zafi da aka gudanar a wajen kasashensu. 

Har ila yau, wannan nasara tana wakiltar wani sabon tarihi na lambar zinari mafi yawa da kasar Sin ta samu a gasar wasannin Olympics da aka gudanar a wajen kasar Sin, wato karin lambobin zinari guda biyu idan aka kwatanta da rawar da ta taka a wasannin Olympics da aka yi a Tokyo a baya. Amma abu mafi daukar hankali ga nasarar da kasar Sin ta samu a wannan fita shine irin rawar gani da ’yan wasa na kasar Sin matasa wadanda aka Haifa bayan shekara ta 2000 suka taka a wannan nasarar da Sin ta samu a gasar Olympics ta Paris, kana suka zama abun alfahari ga kasarsu da iyayensu bisa gudummarwar da suka bayar.  

’Yan wasan motsa jiki na kasar Sin matasa wadanda aka haifa bayan shekara ta 2000 sun yi fice kuma sun kafa tarihi a wannan gasar wasannin Olympics ta Paris ta 2024, wadanda kamar tashin igiyar ruwa a babban kogi, sun dauki hankalin duniya baki daya, sun nuna kwazo, juriya da kuzari a fagen wasa yayin da suka yi fice a birnin Paris cike da kwarin gwiwa da fara’a. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohamed Yahaya)