Kasar Sin Ta Bukaci Philippines Da Ta Dakatar Ayyukan Keta Iyaka A Tsibirin Huangyan
2024-08-14 10:43:12 CMG Hausa
Kakakin harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya Talata cewa, kasar Sin ta bukaci Philippines da ta dakatar da ayyukan keta iyaka da tsokana a tsibirin Huangyan.
Lin ya bayyana hakan ne a lokacin da aka nemi ya yi tsokaci game da kalaman kuskure na baya-bayan nan na shugaban kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos da shugaban hafsoshin sojan kasar ta Philippines Romeo Brawner's dangane da yankin tsibirin Huangyan na kasar Sin.
Lin ya bayyana cewa, tsibirin Huangyan ya kasance yankin kasar Sin a ko da yaushe, kuma kasar Sin tana da ikon mallakar tsibirin Huangyan da sararin samaniya da ruwa dake kusa da ita.
Lin ya ce, sau biyu jiragen saman sojan Philippines sun kutsa cikin sararin samaniyar da ke kusa da tsibirin Huangyan a ranakun 7 da 8 ga watan Agusta, wanda ya yi matukar keta ikon mallakar kasar Sin, kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa da ka'idojin da suka shafi dangantakar kasa da kasa.
Lin ya kara da cewa, sojojin kasar Sin sun dauki halaltattun matakan da suka dace domin mayar da martani, kuma sun gudanar da ayyuka a wurin cikin kwarewa bisa dokokin kasar Sin da dokokin kasa da kasa. (Yahaya)