logo

HAUSA

An kaddamar da dandalin bunkasa noma da yaki da fatara na Sin da sassan Afirka a Kenya

2024-08-14 20:21:52 CMG Hausa

Yanzu haka an kaddamar da wani dandali da ya hallara masu tsara manufofi, da masana kimiyya, da jagororin masana’antu daga Sin da kasashen Afirka, da kuma cibiyar kasa da kasa ta inganta noman masara da alkama ko (CIMMYT), a birnin Nairobin kasar Kenya.

Dandalin wanda zai gudana tun daga jiya Talata har zuwa ranar Juma’a, na da nufin ingiza burin da ake da shi na kyautata harkokin noma, da cimma nasarar samar da isasshen abinci, da shawo kan fatara a yankunan karkarar nahiyar Afirka.

Cibiyar kimiyyar noma ta kasar Sin ko CAAS, da cibiyar CIMMYT ne suka dauki nauyin shirya dandalin, wanda ya tattara mahalarta sama da 100, yake kuma mayar da hankali ga "Sauya tsarin sarrafa cimaka daga albarkatun gona a nahiyar Afirka, ta hanyar kirkire kirkiren kimiyya, da hadin gwiwa sassa mabanbanta". (Saminu Alhassan)