logo

HAUSA

Kasar Sin na tir da harin Isra’ila kan makarantu a Gaza tare da kira da a dakatar da bude wuta

2024-08-14 11:32:13 CMG Hausa

 

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce harin da Isra’ila ta kai makarantun Gaza a makon da ya gabata, ya yi sanadin asarar daruruwan rayukan da ba su ji ba su gani ba. Yana mai cewa Sin na yin Allah wadai da kausasan kalamai.

Fu Cong ya bayyana haka ne yayin wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhu na MDD da ya gudana jiya Talata, inda ya kara da cewa, dakatar da bude wuta nan take shi ne abun da al’ummar Gaza ke bukata cikin gaggawa, kuma ita ce matsayar da kasa da kasa suka cimma.

A cewarsa, ya kamata Amurka wadda ita ce kan gaba wajen samar da makamai ta dauki sahihan matakai na kira ga Isra’ila ta dakatar da ayyukanta na soji a Gaza nan take, tare da dakatar da kisan fararen hula.

Jami’in na Sin ya kara da cewa, wani jawabi na baya bayan nan da wani babban dan siyasar Isra’ila ya yi cewa, “kyale al’ummar Gaza miliyan 2 yunwa ta kashe su, abu ne da ya dace,” abu ne da ba za a lamunta ba. Ya ce yunwa ba zai taba zama makami ba, kuma ba zai yiwu a siyasantar da batun jin kai ba, kana ba zai yiwu rayukan fararen hula ya zama abun da za a yi amfani da shi wajen cimma yarjejeniya ba. (Fa’iza Mustapha)