logo

HAUSA

Cibiyar CDC ta Afirka ta ayyana dokar-ta-baci kan kyandar biri a matsayin barazana ga lafiyar jama’a na nahiyar

2024-08-14 10:46:20 CMG Hausa

 

A jiya Talata ne Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, ta ayyana dokar-ta-baci kan barkewar cutar kyandar biri a Afirka a matsayin Aikin Gaggawa na Lafiyar Jama’a da Tsaron Nahiyar wato PHECS a takaice.

Darakta-janar na Afirka CDC Jean Kaseya ne ya bayyana matakin na PHECS a lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai na musamman ta yanar gizo, game da bullar cutar a Afrika, tare da nuna damuwarsa kan yadda cutar ke saurin yaduwa, musamman daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) zuwa kasashen makwabta.

A cewar shugaban cibiyar, matakin zai taimaka matuka wajen tattara kayan aiki tare da karfafa tsarin sanarwa na kasa da kasa, kana matakin zai tilastawa kasashe mambobin AU su sanar da CDC na Afirka duk matakan kiwon lafiya da aka aiwatar a cikin gaggawa. Ana kuma sa ran za a kara yawan kudade, da kuma tattara kayan aiki a kan barkewar cutar. (Mohammed Yahaya)