Nazarin CGTN ya bayyana yadda wasu mutane a fadin duniya suka soki EU don gane da takkadamar cinikayya tsakaninta da Sin
2024-08-13 14:42:53 CMG Hausa
Domin kare hakkoki da muradun masana’antar samar da motoci masu amfani da makamashi mai tsafta ko EVs da ba da hadin kai ga kokarin duniya na kare muhalli, kasar Sin ta gabatar da kara gaban sashen warware rikici na hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO), bisa matakan da Tarayyar Turai wato EU ta dauka kan motoci masu amfani da sabon makamashi kirar kasar.
Bisa wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar ta intanet, kaso 87.5 na jama’ar da suka shiga nazarin a duniya, sun bayyana cewa, matakin kariyar cinikayya da EU ta dauka, ba gazawa wajen warware takaddamar dake tsakanin bangarorin biyu kadai za su yi ba, har ma da yin mummunan tasiri kan masana’antar kera motoci ta duniya.
Yayin da duniya ke fuskantar kalubale wajen tafiyar da harkokin da suka shafi yaki da sauyin yanayi, motocin EV sun zama wani muhimmin bangare ga kasashen duniya wajen cimma burin rage fitar da hayakin Carbon. Cikin nazarin, kaso 87.96 na mutanen sun yabawa yadda kasar Sin ta dukufa wajen raya masana’antar sabon makamshi kamar ta motocin EV, lamarin da ke bayar da gagarumar gudunmuwa ga tattalin arzikin duniya da ma kokarin duniyar na kare muhalli. Kaso 82.96 kuma, sun soki matakan kariyar cinikayya na EU, wadanda za su gurgunta kokarin kasashen duniya na hada hannu domin yaki da sauyin yanayi.
An fitar da nazarin ne a dandamalin kafar CGTN na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda cikin sa’o’i 24, masu amfani da intanet 12,032 suka bayyana ra’ayoyinsu.